Taron SPD da CDU a birnin Berlin | Labarai | DW | 01.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron SPD da CDU a birnin Berlin

Yau ne a fadar gwamnatin Jamus dake birnin Berlin, a ka fara tantanawa tasakanin tawagogin SPD da CDU, manyan jam´iyu masu ƙawace a gwamnatin Tarayya bisa jagorancin Angeller Merkell.

Mahimman batutuwan da tawagogin 2 ke tantanawa a kai, sun haɗa da, kwaskwarima ga tsarin kiwon lahia, da kuma biyan harajin masu hannu da shuni.

Ɓangarori 2, na fuskantar saɓanin ra´ayoyi, a game da wannan mahimman batutuwa.

Dukkan su, sun amince, da ƙara yawan haraji, da kashi 3 bisa 100, ga ma´aurata da ke samun Euro fiye da dubu 500 a shekara, da kuma mutum ɗaya,da ya mallaki rabin wannan kuɗaɗe a cikin shekara.

To saidai, inda saɓanin ya ke, yan CDU ba su amince ba, wannan haraji, ya hau kan kampanoni, saɓanin SPD.