Taron kolin shugabannin EU a Bratislava | Labarai | DW | 16.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kolin shugabannin EU a Bratislava

Taron farko na shugabannin EU bayan ficewar Birtaniya daga kungiyar

Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai sun fara wani taro na yini guda yau a Bratislava babban birnin kasar Slovakia. l

Taron na fatan samun manufa ta bai daya yayin da ta ke shirin rungumar kaddara da ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar ta EU, a waje guda kuma da sabanin ra'ayi a kan komai kama daga batun shawo kan kwararar yan gudun hijira izuwa batun tattalin arziki.

Shugabanin kasashen 27 sun hallara, sai dai a wannan karon ba tare da Firaministar Birtaniya inda suka yi hoto da aka saba na al'ada.

Shugabannin dai na fatan cewa taron na yini daya zai samar da hanyoyi na tsara sabuwar taswira na hadin kai da kuma ci gaban kungiyar tararayyar Turan.