Taron kolin Chaina da EU | Labarai | DW | 14.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kolin Chaina da EU

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta gana da shugaba Xi Jinping na Chaina, a bangaren taro mafi girman irinsa da aka shirya gudanarwa tsakanin Beijing da EU.

Taron kolin da zai gudana a wannan Litinin ta kafar bidiyo, na zama kololuwar shugabancin karba-karba na EU da a yanzu yake hannun tarayyar Jamus.

Turai dai na neman matsayi tsakanin Beijing da Washington, ga batun kare hakin dan Adam da harkar kasuwanci.

Da farko an shirya gudanar da taron ne tsawon yini uku a birnin Leipzig na nan Jamus amma saboda corona aka mayar da shi na yini guda