Taron da jami’an kungiyar EU suka yi da takwarorinsu na Iran yau a birnin Brussels ya ci tura. | Labarai | DW | 30.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron da jami’an kungiyar EU suka yi da takwarorinsu na Iran yau a birnin Brussels ya ci tura.

Taron da aka shirya yau a birnin Brussels, a can kasar Belgium, tsakanin jami’an kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus, masu wakilcin Kungiyar Hadin Kan Turai da jami’an kasashen Iran, don tattauna batun shirin makamashin nukiliyan da mahukuntan birnin Teheran suka sanya a gaba, ya ci tura. Da yake yi wa maneman labarai jawabi bayan taron ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier ya ce babu wasu sabbin shawarwarin da aka gabatar, sabili da haka, halin da ake ciki dai bai canza da na da ba.

Kafin dai wani taron da kasashe masu kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya za su yi a birnin London, don kago wani matsayi na bai daya da nufin huskantar kalubalantar da Iran ke yi musu, sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleeza Rice ta ce lokaci ya kai ga kai karar Iran gaban Majalisar Dinkin Duniya.