Taro kan sauyin yanayi a Faransa | Siyasa | DW | 30.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taro kan sauyin yanayi a Faransa

Shugabannin kasashe kimanin 150 ne suka hallarci bude taron sauyin yanayi a birnin Paris inda bakinsu ya zo daya wajen warware matsalolin da ke jawo dumamar yanayi a duniya.

Cikin tsauraran matakan tsaro ne dai aka fara wannan taro a yankin Le Bourge da ke birnin Paris, wanda makasudinsa ke zaman lalubo hanyoyi na dindindin na rage gurbata muhalli wanda ke haifar da sauyin yanayi a duniya baki daya. Da ya ke magana wajen bude taron, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya shaidawa shugabannin da ke halartar taron cewar dole ne su tashi tsaye wajen daukar tsauraran matakan kare muhalli cikin hanzari.

Deutschland Gelsenkirchen Kohlekraftwerk Symbolbild Klimawandel CO2

Taron Paris na son ganin an rage hayaki mai guba da ake fiddawa.

Shugaban Faransa Francois Holland da ke karbar bakuncin taron kuwa cewa ya yi an kawo gabar da za a kauracewa yin alkawura kan warware wannan matsala ta gurbata muhalli, dole ne inji shi a kai ga tudun da aka jima ana son dafawa duba da yawan wanda wannan lamari ke shafa da ma illarsa.

Amirka da Indiya da China da ke kan gaba waje fidda hayakin da ke illa ga muhalli ma dai sun ce suna son ganin an kai ga cimma matsaya kan wannan matsala a wannan taron Paris. Shugaba Barack Obama na Amirka ya ce kasarsa na da muradin ganin matsalar ta kau don tuni ma sun bijiro da matakai na rage ta inda ya ce ''a shekaru bakwai da suka gabata mun maida hakali wajen samun makamashi da ake sabuntawa kana nan da shekaru goma za mu rage hayaki mai guba da kashi 27-28 cikin 100.''

USA Texas Symbolbild Klimawandel Dürre

Karancin ruwan sama da ke haifar da fari na daga cikin illar sauyin yanayi.

A daura da wadannan kalamai na Obama, Indiya na ganin kafin a kai ga yin haka dole ne sai an hada karfi da karfe wajen share fage na kawar da abubuwan da ke jawo yin illa ga muhalli musamman ma talauci. China ma dai na da da ra'ayi makamancin wannan, har ma shugabanta Xi Jinping ya ke cewa hannu daya ba ya daukar jinka.

Wannan kalamai na shugaban China ne ma ya sanya Jacob Zuma na Afirka ta Kudu cewar muddin ba kai ga warware wannan matsala ba to duniya za ta dauka cewar manyan kasashe ba sa tausayawa wanda wannan matsala ta fi shafa. Shugaban na Afirka ta Kudu ya ce ''za yi tunanin cewar wasu kasashe ne suka jawo matsalar da gangan kuma ba sa tausayin wanda ta fi shafa.'' Yanzu haka dai hankalin duniya ya karkata kan yadda za ta kaya dangane da fidda matsaya tsayayyiya kan wannan matsala ta dumamar yanayi na da kwanakin 12 da ke tafe.

Sauti da bidiyo akan labarin