Taro kan rikicin Siriya a New York | Labarai | DW | 18.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taro kan rikicin Siriya a New York

Ministan kasashen ketare na Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce ya na fatan taron da za a gudanar a birnin New York na Amirka kan rikicin Siriya, zai sa a shawo kan matsalar a siyasance.

Steinmeier ya bayyana hakan ne bayan da ya isa birnin na New York domin halaratar taron, inda ya ce muhimman matakan da ya kamata a dauka a wajen taron shi ne hanyoyin da za a bi wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a Siriya. Taron dai zai samu halartar kasashe 17 ciki kuwa har da kasashe biyar masu kujerar din-din-din a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.