Tallafi ga ′yan gudun hijira a Jamus | Zamantakewa | DW | 26.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tallafi ga 'yan gudun hijira a Jamus

Kungiyoyin da ke tallafawa 'yan gudun hijira daga kasashen Siriya da Libiya da Iraki da ke fama da rikici, sun bukaci da a rubanya agajin da ake bawa 'yan gudun hijirar da ke Jamus.

Tarayyar Jamus dai na daga cikin kasashen Turai da suka yi shura wajen karbar 'yan gudun hijira daga kasashen da ke fama da tashin hankali inda suka samu matsugunai da kuma aikin yi yayin da a hannu guda sauran jam'ar gari ke zabura wajen tallafawa irin wadannan mutane ko dai da tufafi na sanyawa ko kayan abinci ko kuma shawarwari. Wannan ne ma ya sanya kungiyoyin da ba na gwamnati ba a kasar ke jinjinawa masu bada wannan tallafi. To sai dai duk da wannan Bernd Mesovic da ke zaman mukaddashin kungiyar nan ta agazawa 'yan gudun hijira ta Pro Asylum na ganin idan mutum na da kyau to ya kara da wanka inda ya ce...

"A wannan gaba ya kamata gwamnati ta kara yin hobbasa sannan ta yi amfani da ma'aikata ba wai a gidajen da ake tsugunar da 'yan gudun hijira ba har ma da wuraren da wadanda ke bada tallafi ke gudanar da aiyyukansu domin cimma burin da ake so."

Wani abu har wa yau da kungiyoyi irin na su Mr. Mesovic ke son ganin an aiwatar shi ne curewa waje guda domin masu bada tallafi ga 'yan gudun hijirar su hadu wajen tafiyar da wannan aiki nasu da nufin ganin an kai ga gudanar da aikin agajin cikin tsari maimakon a ce kowa ya fuskanci gabansa, duk kuwa da cewar dodo guda ake yi wa tsafi.