Takaddama kan shugabancin majalisa a Najeriya | Siyasa | DW | 04.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takaddama kan shugabancin majalisa a Najeriya

Jam'iyyar APC ta kasu gida biyu a majalisar, akwai Unity Forum da Like Minds kuma kowanne na jan daga, abin da jam'iyyar adawa ta PDP ke hangen cewa wata kila, ta samu idan ba su hada Kai ba.

A gefe daya dai tuni shugaban kasar ya bada izini na kaddamar da sabuwar majalisa ta takwas a makon gobe, to sai dai kuma can gefe jam'iyyarsa ta APC mai mulki ta gaza kaiwa ga sulhunta tsakanin yayanta game da samar da shugabanci da ake sa ran zai jagoranci majalisa ta takwas tun daga talatar makon gobe. Wani kokari na sulhunta tsakanin a bangaren majalisar zartarwar jam'iyyar dai ya rushe sakamakon takaddamar da ke akwai a tsakanin bangarorin jam'iyyar guda biyu da kowane ke jan daga.

A gefe daya dai akwai Unity Forum dake samun jagorancin senata Ahmed Lawal da ke zaman dan takara daya tilo na bangaren daga sashen arewa maso gabashin kasar, a yayin kuma da daya barin na kungiyar Like Minds ke samun shugabancin Bukola Ahmed Saraki dake zaman dantakarar kujerar ta shugabancin majalisar daga arewa ta tsakiya.

'Yan takaran shugabancin majalisar

Duk da cewar dai shugabancin jam'iyyar yafi karkata zuwa Ahmed Lawal da ke zaman mafi tsufa a cikin zauren ya zuwa yanzu, da kuma daga dukkan alamu ke da karancin buri a siyasa, Bukola Saraki na takama da sanayya ta siyasa da ma goyon bayan tsoffafin gwamnonin dake cikin majalisar da kuma ke fatan samun daya a cikinsu ya jagoranci majalisar mafi tasiri. To sai dai kuma a fadar Ahmed Lawal takarar ta sa na da ruwa da tsaki da kokari na ceto yankin nasa cikin hali na ukuba da rashin cigaban da rikicin ta'addancin kasar ya haifar ya zuwa yanzu.

Niger Buhari Issoufou

Kafin shugaba Buhari ya fara ziyara a Nijar da Chadi ya ba da izini kafa jagorancin majalisar ta 8 a kasar.

Daga dukkan alamu APC na da sauran aiki a kokari na daidaita tsakanin da nufin tabbatar da samar da shugabanci karbabbe hgun kuwa. Irin wannan rikici ne dai ya zamo dan bar rikirkita harkoki cikin majalisar dattawan da ta zauna ta kalli shugabbani har guda Hudu a tsawon shekaru Hudu da farkon fari. Abun kuma da a fadar Senata Ali Ndume dake bangaren na 'yan Like Minds ya sanya ba za su amince da duk wani kokari na tilasta shugabanci kansu a yanzu ba.

Martanin 'yan adawa

A bangaren PDP ta adawa wajen shigar sauri da kila samar da shugabancin na gaba. Banbancin da ke tsakanin jam'iyyun biyu dai na zaman dattawa 10 tsakanin APC mai 59 da kuma yar uwarta PDP dake da 49. duk da cewar dai kakakin PDP ya ce basu da wannan buri a tunanin Senata Barau Jibrin da ke zaman daya a cikin sabbabin zabbabun tsoma bakin APC da nufin warware rikicin na zama wajibin dake akwai da nufin kaucewar tsagar da kandagaren PDP ke iya fadawa a ciki. Abun jira a gani dai na zaman mafitar rikicin ga APC dake da kwanaki Hudu domin warware matsalar da ta dauke makonni kusan Shida ya zuwa yanzu.

Sauti da bidiyo akan labarin