Taƙaddama tsakanin Majalisar ƊInkin Duniya da Iran. | Labarai | DW | 26.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taƙaddama tsakanin Majalisar ƊInkin Duniya da Iran.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta shiga takon tsaƙa da Iran game da harkar sadarwa.

default

Ban Ki Moon tare da wani jami'i na Majalisar Ɗinkin Duniya

Hukumar sadarwa ta Majalisar Ɗinkin Duniya(UIT) ta buƙaci ƙasar Iran da ta kawo ƙarshen takunkumi da ta saka wa kafofin yaɗa labarai na waje, bayan da ta birkita taurarun ɗan adam da ke watsa shirye-shiryen kafofin ƙasashen waje a ƙasar ta Iran. Ministocin harkokin waje na ƙasahen Tarayyar Turai da ke taro a birnin Brussels sun yi tir da allah wadai da matakin da ƙasar ta Iran ta ɗauka wanda ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da akan aikin sadarwa da Iran ɗin ta sa hannu akai. Gidajen rediyo dai irin su Deutsche Welle da BBC da sauran tashoshin telebijan da ake kamawa a da a ƙasar ta Iran a yanzu ba a kallonsu ba a kuma saurarensu. Wannan doka ta ƙasar ta Iran ta zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke bukin zagayawar cikon shekara na juyin-juya-hali na gwamnatin Islama da ake yi a ƙasar wanda 'yan adawar ke amfanin da shi domin kiran jama'a da su shiga zanga-zanga.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Halima Abbas