Sojojin Amirka za su taimaka kan yaki da Boko Haram | Siyasa | DW | 15.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sojojin Amirka za su taimaka kan yaki da Boko Haram

Jama'a sun bayyana ra'ayoyinsu kan batun tura sojojin Amirka zuwa kasar Kamarun domin su taimaka wa yaki da kungiyar Boko Haram.

Bayanai dai sun nunar cewa tuni wata tawaga ta Sojojin kasar Amurkan suka fara isa kasar Kamaru a wani mataki na cika alkwarin da Shugaban Amirka Barack Obama ya yi na bada agaji don yaki da ayyukan kungiyar Boko Haram wacce ta yi mubaya’a ga kungiyar IS da yanzu kuma ake kiran ta da suna Daular Musulunci a nahiyar Afirka ta Yamma. Ana sa ran Sojojin 300 ne za su isa kasar ta Kamaru da kuma wasu sassan nahiyar domin yin aikin bada shawarwari da horaswa gami da ayyukan leken asiri, sannan kuma za su je da makamai domin taimaka wa kasashen Najeriya da Chadi da Nijar da ita kasar ta Kamarun yaki da Boko Haram.

Sojojin Amirka sun fara isa kasar Kamarun

Wannan mataki na kasar Amurka na tura Sojoji domin yaki da Boko Haram ya haifar da martani daga ‘yan Najeriya da ma kasar ta Kamarun, inda wasu ke maraba da matakin wasu kuma keganin ba shi da wani amfani a wannan lokacin. Masu murna da matakin dai na ganin halin da yankunan suka samu kansu na tabarbarewar tsaro akwai bukatar samun gudunmowa ta ko wane hali daga ko'ina kuma musamman kasar Amurka da ke da karfi da dabarun yaki.

Ra'ayoyin al'umma dai sun bambanta

Sai dai ra’ayi ya sha ban-ban inda wasu ke ganin shigar kasar Amurka cikin wannan yaki a wannan lolakci bas hi da wani alfanu tun da dakarun Najeriya su na samun nasara. Kungiyar Boko Haram wacce tayi mubaya’a ga Kungiyar IS ta addabi kasashen Kamaru da Chadi, Nijar da kuma Najeriya inda ta hallaka dubban mutane a cikin shekaru shida abin da ya sa kasashen da ke yankin tafkin Chadi suke neman taimakon manyan kasashen duniya domin magance ayyuakan kungiyar a yanki.

Sauti da bidiyo akan labarin