Shugabannin kasashen Jamus da Indiya sun gana | Labarai | DW | 06.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin kasashen Jamus da Indiya sun gana

Kasashen Jamus da Indiya sun amince da sabbin matakai kan kasuwanci da makamashi gami da tsaro.

Kasashen Jamus da Indiya sun saka hannu kan sabbin tsare-tsare 18 na kasuwanci, da makamashi, da kuma tsaro.

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel da Firaminista Narendra Modi suka amince da sabbin tsare-tsaren yayin da Merkel ta ke ci gaba da ziyara a birnin New Delhi na kasar ta Indiya. Modi ya kuma nuna amincewa da sake shiga tattaunawa bisa yarjejeniyar kasuwanci da babu shinge da kungiyar Kasashen Turai, wadda ya dakatar a farkon wannan shekara ta 2015.