1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za mu ciyar da EU gaba inji Merkel

Abdullahi Tanko BalaSeptember 16, 2016

Taron kolin EU ya amince da sabuwar taswirar ci gaba

https://p.dw.com/p/1K3wp
Slowakei EU Gipfel in Bratislava Gruppenfoto
Hoto: Reuters/L. Foeger

Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai a karshen taron kolin da suka gudanar a Bratislava babban birnin kasar Slovakia sun amince da sabuwar taswira da za ta ciyar da kungiyar gaba.

Taswirar dai ta kunshi hanyoyi da kuma dabarun inganta amincin al'umma da kuma yarda a tsakanin kasashen kungiyar bayan sakamakon ba zata na kuri'ar raba gardamar da Birtaniya ta kada na ficewa daga kungiyar.

Jakadu a taron sun ce tattaunawar ta gudana cikin nasara.Kasashen sun jaddada kudirin yaki da ta'addanci don tabbatar da tsaron nahiyar Turai.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi tsokaci:

" Ta ce kada yi tsammanin a taro guda za'a warware dukkan matsalolin nahiyar Turai. Muna cikin wani yanayi na tsaka mai wuya, to amma wannan dama ce ta nuna cewa ta hanyar daukar mataki, za mu iya inganta lamura musamman ta fuskar tsaro a cikin gida da waje da kuma yaki da ta'addanci."