Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ya yi murabus | Labarai | DW | 10.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ya yi murabus

Rahotannin da ke shigowa daga Chadi na cewar shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Michel Djotodia ya sauka daga mukaminsa na shugabancin kasar.

Mr. Djotodia ya bayyana yin murabus din ne yayin taron da ake na kasashen tsakiyar Afrika a kasar a Chadi, wanda ya maida hankalinsa wajen lalaubo hanyoyin warware rikcin kasar wanda ya jawo rasuwar mutane da dama.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya rawaito cewar nan gaba kadan ne ake sa ran fara tattaunawa a birnin Bangui na Jamhuriyar ta Afrika Tsakiya da nufin fidda wanda zai maye gurbin shugaban kasar.

An dai zarge Mr. Djotodia ne da kasa kawo karshen rikici tsakanin Kirista da Musulmi, batun da ya sanya shugabannin yankin matsa masa lamba ta yai murabus.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu