1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Issoufou ba zai tsaya takara a 2021 ba

Mouhamadou Awal Balarabe GAT
August 16, 2018

A tattaunawarsa da DW bayan ganawa da Merkel kan matsalar bakin haure, Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar ya jadadda aniyar sauka daga mulki bayan karewar wa'adin mulkinsa na biyu a shekara ta 2021.

https://p.dw.com/p/33HUy
Deutschland - Issoufou Mahamadou, Staatspräsident Niger im DW-Interview in Berlin
Hoto: DW/N. Haase

A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar Rediyo da talabijin ta DW bayan ganawarsa da shugabar gwamnatin Jamus, Shugaba Issoufou ya nemi karin tallafin kudi don yaki da matsalar tsaro da ke addabar Nijar da kawayenta. Kana ya ce a shirye yake ya bada gudunmawa wajen dakile kwararar bakin haure zuwa Turai matukar kasarsa za ta amfana. 

Kasashen Yamma na taimaka wa Nijar tsayawa a kan kafafunta a fannin dimukuradiyya, inda EU ta ba da miliyan dubu na Euro yayin da Amirka ta bayar da miliyan 400 na Dalar Amirka bisa sharadin sakar wa 'yan adawa marar gudanar da harkokinsu. Sai dai Issoufou ya nesanta gwamnatinsa da gudanar da salon mulkin kama karya, yana mai cewa tana mutunta hakkin fadar albarkacin baki da na banbancin akidar siyasa tare da mutunta kundin tsarin mulki. Wannan ne ya sa ya jaddada cewar ba zai sake tsayawa takara ba idan wa'adin mulkinsa na biyu ya kare.

"A matsayina na shugaban kasa, wa'adi biyu nake da izinin yi. Na yi wa'adin farko da ya kare a shekarar 2016, sannan an sake gudanar da zabe da na lashe. Tun da kundin tsarin mulki ya bayyana cewa shugaban kasa ba zai iya wa'adin mulki uku ba, ba zan sake tsayawa takara a zaben 2021 ba. Dan kama karya ba zai iya yanke wannan shawara ba. Mun yi imanin cewar dimukuradiyya da tsaro da ci-gaban kasa abubuwan uku ne da ba a iya raba su, saboda haka ne muke aiki a kan fannonin uku."

Deutschland Merkel trifft Mahamadou
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Hirschberger

Sai dai kwararar bakin hauren Afirka zuwa Agadez na Nijar da nufin tsallakawa Turai ta ko halin kaka na neman zama barazana ga zaman lafiyar kasar. Dama Jamus da ma sauran kasashen Turai na neman hadin kan Nijar don yaki da kwararar bakin hauren Afirka. Hasali ma Jamhuriyar Nijar ta kasance kasa daya tilo da ta amince da kafa cibiyar tsugunar da bakin haure da tantance su domin su shiga Turai ta hanyar da ta dace. Amma kuma Shugaba Mahamadou Issoufou ya ce yana bada hadin kai don kare muradin kasarsa da kuma wasu karin dalilai.

"A matsayina na daya daga cikin shugabannin Afirka, ba zan yarda matasan Afirka su rika mutawa a hamadar sahara da tekun Bahar-Rhum ba. Dalili na biyu kuma ya shafi tsaro saboda masu safarar bakin haure zuwa Libiya na dawo Nijar da makamai, lamarin da ke haddasa matsalar tsaro. Wadannan muhimman dalilan ne suka sa Nijar ta tsara shirin yaki da safarar bakin haure da muka aiwatar cikin nasara, domin mun rage yawan bakin hauren. A shekara ta 2016 bakin haure kusan dubu 100 ne ke bi ta Nijar, amma yanzu ba sa fin dubu 10 a shekara. A takaice dai ba wai don Jamus ko Turai sun bukace mu ba ne muke wannan aiki, amma muna da dalilan kanmu da suka kaimu ga daukar wannan mataki." 

Deutschland - Issoufou Mahamadou, Staatspräsident Niger im DW-Interview in Berlin
Hoto: DW/N. Haase

Jamhuriyar Nijar na taka muhimmiyar rawa a fannin yaki da ta'addaci musamman a yankin Sahel da kuma kasashen da ke kewayen tafkin Chadi, inda Boko Haram ke aikata ta'asa, lamarin da ya kasance a sahun gaba na ajandar tattauwar Shugaba Issoufou da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel. Duk da irin taimakon kayan yaki da horo da Nijar take samu daga Jamus don magance matsalar tsaro da ke addabar ta, amma kuma Shugaba Mahamadou Issoufou ya ce akwai bukatar samun gudunmawa daga Majalisar Dinkin Duniya don cimma nasara.

"Wannan yaki da muke yi ta hanyar hada karfi da karfe tsakanin kasa da kasa a Sahel da yankin tafkin Chadi, na bukatar gudunmawar Majalisar Dinkin Duniya. Wannan ne ya sa a tattaunawarmu da shugabar gwamnatin Jamus na nemi karin taimakon Kungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya don samun kudin karfafa ayyukan rundunar hadin gwiwa ta G5 Sahel. Kamar yadda kuka sani mun samu kudin gudanar da ayyukan shekarun farko, amma da yake yaki da ta'addanci na fiye da shekara guda, muna neman kafa ta samun karin kudi."

Cikin raha ne dai shugaban na Nijar ya kammala hirar da DW.