1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Buhari ya gana da gwamnonin APC

Ubale Musa ATB(AMA
February 3, 2023

A kokarin dinke barakar da ta kunno kai a tsakanin wasu 'yan jam'iyyar APC kan batun sake fasalta takardar kudi ta naira a Najeriya, shugaban kasa ya gana da wasu gwamnoni.

https://p.dw.com/p/4N4iH
Hoton shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a yayin wata ganawarsa a Katsina
Hoton shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a yayin wata ganawarsa a KatsinaHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

A cigaba da kokarin kare rikicin da ke barazana ga makomar jam'iyar APC mai mulkin Najeriya, gwamnonin jam'iyyar 22 sun gana da shugaban kasa da nufin gano bakin zaren warware matsalolin da ke tattare da sabon tsarin fasalta kudin Najeriya da ya janyo kace-nace. A tozalin da gwamnonin suka yi da shugaba Muhammadu Buhari, a karon farko wasu gwamnonin da ke zargin wasu masu fada a ji a fadar gwamnatin kasar da kokarin cika burinsu na kauda masu tsintsiya daga mulki a yayin babban zaben da ke tafe, ta hanyar amfani da batun sauyin kudin naira da ke ci gaba da tada kura.

Karin Bayani: An tsawaita wa'adin karbar tsoffin kudi a Najeriya

Ganawar da ta dauki awowi kusan biyu ta kare tare da alkawarin shugaban kasar na shaida wa gwamnonin cewar yana shirin sauraron bangarorin da ke rikicin kafin yanke hukuncin da yake ganin ya dace a matsayin mafita ga rikicin da ya dau sabon fasali irin na siyasa. Babbar fargabar da ta mamaye zukatan wasu kusoshin gwamnatin Muhammadu Buhari, ita ce jam'iyyar fuskanci fushi daga masu zabe a fadin kasar bayan bijiro da sabon tsarin na sake fasalin kudin Najeriya da ake dada kallo tamkar asara ga wasu miliyoyin 'yan kasar a halin yanzu.

Hoton sabbin kudin Naira da aka kaddamar a Najeriya
Hoton sabbin kudin Naira da aka kaddamar a NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

Sai dai a fadar gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, "Abun da ke faruwa a yanzu, baya da wani tasiri ga tunanin 'yan Najeriya masu kada kuri'a."

Karin Bayani: Shirye shiryen zaben Najeriya ya kankama

Sannu a hankali rikicin sabon kudin Najeriya na neman rikidewa ya zuwa ga na siyasa mai zafi, wanda magoya bayan Shugaba Buhari ke zargin gwamnan jihar Kaduna da kokari na neman sabon ubangida. A baya dama Gwamna el-Rufa'i ya yi fada da Atiku Abubakar a lokacin da yake neman hada inuwa da Obasanjo, kafin daga baya ya zagi Obasanjon a kokarinsa na neman shiri da shugaban da ke mulkin Najeriya a yanzu, duk da yake gwamna el-Rufa'i ya nuna cewa, zarge-zargen hira ce kurum irin ta taburin mai shayi.