Shirin zaben shugaban kasa a Najeriya | Siyasa | DW | 12.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin zaben shugaban kasa a Najeriya

Tsohon shugaban kasa na mulkin soji janar Muhammadu Buhari ne mutumin da zai kalubalanci Shugaba Goodluck Jonathan a zaben shekara ta 2015 mai zuwa a Najeriya.

A ranar Alhamis ce (11.12.2014), babbar jam'iyyar adawa ta APC ta zabi Muhammadu Buhari a matsayin dan takararta. Bayan da a ranar Laraba jam'iyyar PDP da ke mulki ta tabbatar da takarar shugaban kasa Goodluck Jonathan. Manyan 'yan takarar da za su fafata da juna a zaben neman kujerar shugabancin Najeriya na watan Fabrairun shekarar ta 2015 ba baki ba ne, domin sun taba kalubalantar juna a zaben 2011, zaben da Jonathan ya lashe. Shin ko yaya zaben na wannan karon zai kasance, shin ya ya za a iya kimanta karfin 'yan adawa musamman babbar jam'iyyar adawa ta APC? Heinrich Bergstresser masani ne na harkokin siyasar Najeriya, ya yi karin haske:

Heinrich Bergstresser

"Ka mu manta APC da ta samo asali daga jihohin Yarbawa amma ta samu karbuwa a sassa daban daban na kasar. Tare da Buhari jam'iyyar ta samu karbuwa arewcin kasar. Amma ka da mu manta zaben shugaban kasa ya bambamta da na gwamnoni ko 'yan majalisar jihohi ta tarayya. Saboda haka ba abu mai sauki ba ne ga jam'iyyar APC da Buhari su lashe zaben shugaban kasa. Amma jam'iyyar za ta taka rawar gani a zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki, wanda haka zai ba ta damar shiga cikin gwamnati."

Ba abu mai sauki ba ne a kasashen Afirka shugaban da ke kan karagar mulki ya fadi a zabe. Musamman kasancewa hukumomin gwamnati na hannunsa kuma sau da yawa ana amfani da jami'an tsaro ana tursasa wa 'yan adawa. An ga dai misalai a matakin zaben jihohi a Najeriya, yadda jam'iyyar PDP ta shugaba Jonathan ta yi amfani da wannan karfi don cimma muradunta, inji Heinrich Bergstresser masanin harkokin siyara Najeriya kuma tsohon daraktan gidauniyar Friedrich-Nauman a Najeriya, in da ya ba da misali da zaben gwamnan jihar Ekiti ya na mai cewa:

"A lokacin zaben jihar Ekiti, gwamnati ta yi amfani da karfi fiye da kima a kan magoya bayan APC. Dole mu kwana da sanin cewa a cikin makonni masu zuwa na yakin neman zabe, tursasawa har izuwa cin zarafin 'yan adawa zai zama ruwan dare a Najeriya."

A zaben shekarar 2011 daruruwan mutane suka rasu sakamakon tashe-tashen hankula da suka biyo bayan zaben. A wannan karon ma ana fargabar sake aukuwar wannan lamari, musamman yanzu da sha'anin tsaro ya tabarbare sakamakon ayyukan tarzoma. Saboda haka batun tsaro ke daukar hankali a zabe mai zuwa. Kawo yanzu matakan da Jonathan ya dauka da nufin murkushe 'yan tarzoma sun ci tura. To sai dai a cewar Heinrich Bergstresser shi ma Buhari na jam'iyyar APC bai gabatar da wani shiri mai gamsarwa ba.

"Wannan gwamnati ta gaza kawo karshen ayyukan masu ta da kayar baya a Najeriya. To amma shi ma Buhari zai kasance ne da hukumomin tsaro iri daya kamar Jonathan da mashawartansa. Ba za a samu wani canji na a zo a gani ba. Kuma ban ji ya gabatar da wani shiri da zai kawo karshen ayyukan Boko Haram ba."

Sauti da bidiyo akan labarin