Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji martanin 'yan Najeriya kan jawabin shugaba Buhari, a Nijar dattin leda na kasancewa babbar annoba da ke haddasa matsalar gurbacewar muhalli.
Rundunar hadin gwiwar Najeriya da Nijar sun yi nasarar halaka akalla mayakan jihadi 55 a yayin wani samamen hadin gwiwa da suka kai mabuyarsu a garin Arege.
Gomman mata ne aka yi garkuwa da su a Kamaru, zargin da ya hau kan 'yan awaren nan na yankin rainon Ingilishi na da ke gwagwarmayar neman ballewa.
Bisa taimakon Kungiyar Tarayyar Turai, kwararru a harkar tsaro na kasashe 10 na Sahel da Sahara na duba rawar da fararen hula za su iya takawa a yaki da ta'addanci.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya kaddamar da matatar man fetur ta Dangote a Ijebu Lekki a birnin Legas, matatar da ke iya sama wa sama da mutum dubu 100 aikin yi.