Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin bayan Labaran Duniya, akwai rahotanni da suka hadar da na halin da ake ciki a siyasar Najeriya. Akwai sauran rahotanni da kuma shirye-shiryen da muka saba gabatar muku.
Wasu kasashen Afirka na ci gaba da kaurin suna a fannin cin-hanci da karbar rashawa ko sama da fadi da dukiyar kasa, inda Somaliya da Sudan ta Kudu suka kasance a matsayin farko.
Harkokin yau da kullum na Nijar da ke makwabtaka da Najeriya na tafiyar hawainiya sakamakon zaben da ya gudana. A Maradi harkokin kasuwanci da zirga-zirgar jama'a sun sukurkuce saboda rufe kan iyakar kasashen biyu.
An fara taron koli tsakanin gwamnatin Amirika da wasu shugabannin kasashen nahiyar Afrika 49, lokaci da gwamnatin Shugaba Joe Biden take neman hanyoyin da za ta rage karfin tasirin kasashen Chaina da Rasha a Afirka.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran agajin gagawa don ceto rayukan kananan yara miliyan 30 da ke fama da tamowa a wasu kasashen da ke fama da karancin abinci.