A cikin hirin za a ji cewa Tawagogin manyan jami’an gwamnatin Aljeriya da Libiya na ziyarar aiki a Nijar a wani mataki na karfafa huldar kasashen ta fannonin diplomasiyya da kuma tattalin arziki da tsaro. A Najeriya kuwa bangarori dabam-dabam ne ke mayar da martani kan matakin gwamnati na ba wa ma'aikatan da matansu suka haihu hutu na tsawon mako biyu.