Shela ta yin hakuri da juna a Jamus | Labarai | DW | 11.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shela ta yin hakuri da juna a Jamus

Wakilai na ƙungiyoyin daban-daban a nan Jamus haɗe da na ƙungiyoyin addinai sun yi kira da murya ɗaya wajen ganin an akawo ƙarshen nuna wariyar jinisi tare da yin hakurin da juna a tsakainin al'umma.

Sanarwar wacce ƙungiyoyi da dama suka rataɓa hannu a kai na da zumar kare hakki da mutunta yanci bil adama, tare da tabbatar da sahihin tsari na demokaraɗiya a duniya da kuma walwalar jama'a.Musammun tare da ƙaddamar da kampe na yin sassauci a kan muhawara mai zafi da ake tafkawa kan butun ba da mafaka ga 'yan gudun hijira a nahiyar Turai. Kana kuma sanarwa na ƙara jan hankali a kan masu tsatsaura ra'ayi da ke farma 'yan gudun hijira wanda a dalilin haka za su iya fuskantar tuhuma a gaban kotu.An shirya haɗin gwiwar waɗannan ƙungiyoyi na ƙwadogo da na addinai da kuma na sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu za su ƙaddamar da wannan shela ta yin hakuri da juna a yau a birnin Berlin.