Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Helmut Schmidt wanda ya rike mukamin shugaban gwamnati Jamus daga 1974 zuwa 1982 ya dade ya na fama da rashin lafiya, kafin ta tsananta a kwanakin baya-bayan nan.
Tsawon watanni ana jiran bayanan da gwamnatin Jamus za ta fitar kan manufofinta na tsaro. Sai dai kuma an sake dage fitar da bayanan. Abin da ya janyo cece-kuce a cikin gwamnatin.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai kai ziyarar aiki yankin kahon Afirka a ranar Alhamis domin inganta dangantakar kasashen Jamus da Habasha da duba hanyoyin da za a kawo karshen rikicin sojoji a Sudan.
Jam'iyyar Social Democrats ta sha kaye a zaben da aka gudanar na jiha a Berlin, inda kiyasin kafafen yada labarai ya nunar da cewa SPD din ce ta zo ta biyu a zaben.
Shugaban gwamnati Olaf scholz ya tabbatar da nadin dan siyasar jam'iyyar SPD kuma ministan cikin gida na jihar Lower Saxony, Boris Pistorius a matsayin sabon ministan tsaro.