Helmut Schmidt na daga cikin 'yan siyasa da ake gani da kima a Jamus. ya rasu a ranar 10 da watan Nuwamban 2015.
An haifeshi a 1918 a birnin Hamburg, ya fara rike mukamin ministan kudi da na tsaro kafin ya shugabanci gwamnatin Jamus daga 1974 zuwa 1982. A wa'adin mulkinsa ya nuna rashin sani da sabo kan masu tsaurin ra'ayi.