Tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Schmidt ya mutu | Labarai | DW | 10.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Schmidt ya mutu

Helmut Schmidt wanda ya rike mukamin shugaban gwamnati Jamus daga 1974 zuwa 1982 ya dade ya na fama da rashin lafiya, kafin ta tsananta a kwanakin baya-bayan nan.

Tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Schmidt mai shekaru 96 a duniya ya mutu a wannan Talatar sakamakon rashin lafiya mai tsanani. Ofishinsa da ke birnin Hamburg ne ya bayar da wannan sanarwa.

Mista Schmidt ya rike mukamin shugaban gwamnatin Jamus daga shekarar 1974 zuwa da 1982 karkashin wata gamayya da ta hada jam'iyyarsa da ke da matsakaicin ra'ayin gurguzu da kuma ta FDP da ke da ra'ayin jari hujja.