Samamen 'yan sanda a Jamus | Labarai | DW | 01.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Samamen 'yan sanda a Jamus

Jami'an tsaro a Jamus sun cafke wani dan asalin kasar Tunusiya da ake zargi da saka mutane cikin kungiyar 'yan ta'addan IS.

Samamen 'yan sanda a Jamus

Samamen 'yan sanda a Jamus

Mai kimanin shekaru 36 a duniya, jami'an tsaron sun cafke shi ne a tsakiyar kasar ta Jamus da sanyin safiyar wannan Laraba. Babban mai shigar da kara na birnin Frankfurt cibiyar bankuna nahiyar Turair, Alexander Badle ya nunar da cewa, an cafke mutumin ne yayin wasu samame har 45 da aka kai wasu gidaje da guraren kasuwanci da kuma wasu masallatai biyu a jihar Hasse, kana an kama wasu da ake zargi har mutum 16 da shekarunsu suka kama daga 16 zuwa 46 kuma ana gudanar da bincike a kansu.