1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gudanar da babban zabe a kasar Saliyo

June 23, 2023

Kimanin 'yan takara 13 ne ke neman kujerar shugaban kasa a Saliyo. Shugaba mai ci Julius Maada Bio na jam'iyyar SLPP da kuma Samara Kamara na jam'iyyar APC, su ne 'yan takarar da suka fi daukar hankali.

https://p.dw.com/p/4Sz8x
Saliyo | Shugaban Kasa | Julius Maada Bio | Tazarce
Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio na son yin tazarceHoto: Ali Balikci/AA/picture alliance

Shugaba Julius Maada Bio mai shekaru 59 na neman wa'adi na biyu na zangon mulkin shekaru biyar. A zaben shekara ta 2018 Bio ya kayar da abokin hamayyarsa Samara Kamara da sama da kaso 52 cikin 100 na kuri'un da aka kada, inda shi kuma Kamara ya samu sama da kaso 48 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Kamara dai na fuskantar zarge-zargen cin-hanci da rashawa na badakalar kwangila daga wani kamfanin New York, sai dai kuma ya ce yana cike da fatan farfado da tattalin arzikin Saliyo. Sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, Bio na fuskantar suka daga bangarori da dama. Matsalar tattalin arziki, ta sake ruruta wutar rikici a Saliyo, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da jami'an tsaro.

Saliyo | Shirin Zabe | Julius Maada Bio | Samura Kamara
Shirye-shiryen zabe a kasar SaliyoHoto: Saidu BAH/AFP/Getty Images

Wasu na korafin cewa, akwai bukatar Shugaba Bio ya yi murabus. Wasu dai na hasashen cewa akwai yiwuwar a dage zaben na shugaban kasa da 'yan majalisun dokoki sakamakon bukatar bukatar jam'iyyar adawa ta APC na a dage zaben har sai an warware takaddama da kuma korafe-korafen da suka gabatar. Babu dai hasashen wanda zai lashe zaben shugaban kasar na Saliyo a karon farko, sai dai kawai ace za'a fafata tsakanin manyan bangarorin da ke kan gaba. Ko ma waye ya lashe zaben, zai fuskanci manyan lakubale da suka hadar da batun farfado da tattalin arzikin da rashin ayyukan yi a tsakanin matasa da batun ilimi da kiwon lafiya har ma da korafin mata na rashin samun wakilci a al'amuran da suka shafi siyasar kasar.