Sakamakon zaben Najeriya na wasu jihohi | Labarai | DW | 30.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaben Najeriya na wasu jihohi

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC na kan tattara sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar Asabar din da ta gabata.

Daga sakamakon da aka bayyana ya zuwa yanzu dai Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP ya yi nasara a jihohin da suka hada da Ekiti da Enugu da Abuja da Nassarawa.

Shi kuwa Janar Buhari Muhammadu Buhari mai ritaya ya samu nasara a jihohin da suka hada da Kogi da Osun da Ogun da Ondo da Oyo.