Rikicin yankin gabas ta tsakiya | Siyasa | DW | 29.06.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin yankin gabas ta tsakiya

Dakarun Izraela sun kaddamar da hare hare da jiragen yaki akan wata mota da akace na dauke da babban jamiin kungiyar Jihad Islami a zirin Gaza.Majiyar jamian palasdinawa na nuni dacewa,jamiin ya tsira da ransa daga wannan hari na Izraela akan motar dayake tafiya ciki.Dakarun Izraelan dai sun tabbatar da kaddamar da har akan motar,sai dai basu bayanin wanda ke cikinsa ba.Tun da safiyar yau nedai dakarun Izraelan sukyiwa ministoci da yan majalisar dokokin daga jammiyar hamas mai mulki kawanya,a zirin gazan.Wannan na bangaren somame da Izraelan ta kaddamar a yankin na palasdinawa ,domin bukatar sakin sojinta da palasdinawan ke garkuwa dashi.Kawo yanzu dai an shiga ran ata 4 kenan ,da jibge tankunan yaki da dubban mayakan izraelan a kann iyakar gaza ta arewaci.Bugu da kai an tsinci gawar wani matashi bayahude mai shekaru 18 da haihuwa a kusa da Ramallah.

 • Kwanan wata 29.06.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BtzX
 • Kwanan wata 29.06.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BtzX