Rikici ya yi zafi tsakanin Kwankwaso da Ganduje | Siyasa | DW | 27.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikici ya yi zafi tsakanin Kwankwaso da Ganduje

An kakkabe hannun tsakanin tsohon gwamna daga shugabancin jam'iyyar a Kano an kuma maye gurbinsa da masu goyon bayan gwamna mai ci, lamarin da ya kara harzuka 'yan Kwankwasiya har ta kai wasu na fucewa daga jam'iyyar.

Gouverneur Kwankwaso besucht Baustelle in Kano Nigeria (DW/T. Mösch)

Kwankwaso a hagu da Ganduje a dama lokacin mulkinsu na baya

Biyo bayan wutar rikicin shugabanci da ta dade ta na ruruwa a jam'iyyar APC a Kano, a makon jiya dai uwar jamiyyar ta kasa ta tabbatar da shugabancin riko a hannun Injiniya Yahaya Bashir Karaye, wanda ke goyon bayan tsagin Gandujiya a jihar, wannan mataki dai shi ne ke tabbatar da dakatar da Umar Haruna Doguwa daga shugabancin jam'iyyar lamarin da ke nuni da cewar an kakkabe hannun tsagin Kwankwasiya daga shugabancin jamiyyar a Kano an kuma maye gurbinsa da masu goyon bayan Gandujiyya, lamarin da ya kara harzuka 'yan Kwankwasiya har ta kai wasu na fucewa daga jam'iyyar tare da yin kakkausan lafazi ga shugabancin jam'iyyar da suke ganin bai yi musu adalci ba.

Shi ma madugun darikar ta Kwankwasiya tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya aiko da sako ga magoya bayansa, ya na mai nuna takaici bisa wannan al'amari. Tun bayan daukar wananan mataki tsagin Kwankwasiya a jihar Kano ya gabatar da wani taron magoya baya har ma an jiyo na hannun daman Sanata Kwankwaso comrade Aminu Abdulsalam na cewar sun yi Allah wadai da wannan dauki saka da aka yi musu.

Nigeria Oppositionspartei APC (DW/K. Gänsler)

Alamu na nuna kullalliya a jam'iyyar ta APC a Kano

To amma masana shari'a irinsu Barista Audu Bulama Bukarti na da imanin cewar sauke Doguwa ya ci karo da kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC dan haka yake cewar akwai kitso da kwarkwata.

Da yammacin nan dai gwamnatin Kano ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar comrade Muhd Garba, ta mayar da martani cikin wani taron manema labarai da suka gabatar, haka kuma tun da fari gwamnatin Kano ta lashi takobin daukar matakin ladaftarwa a kan Sanata Kwankwaso matukar bai nemi gafarar Shugaba Muhammadu Buhari ba, bisa zarginsa da ya yi da hannu cikin wannan abu da suka ce murdiya ne aka yi musu, wannan al'amari ne ke ci gaba da dumama yanayin siyasar Kano, kuma gashi yazo ne kwanaki hudu kacal suka rage a gabatar da gangamin tarbar Kwankwaso a Kano, lamarin da shi ma ake ganin zai karawa yanayin siyasar zafi sosai.

Sauti da bidiyo akan labarin