1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Rasha tamayar wa da Trump martani

Zulaiha Abubakar
July 12, 2018

Fadar mulki ta Kremlin ta yi watsi da zargin da shugaban kasar Amirka Donald Trump ya yi in da ya bayyana cewar kasar Jamus ta dogara ne da Rasha kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Dmitry Peskov ya sanar a yau Alhamis.

https://p.dw.com/p/31LPn
Donald Trump und Wladimir Putin
Hoto: picture alliance/A. Lohr-Jones/A. Astafyev/CNP POOL/Sputnik/dpa

Ya kuma kara da cewar shimfida bututun da ke kai wa Jamus iskar gas daga Rasha kai tsaye ya samo asali ne sakamakon yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen biyu.

 

A halin yanzu alamu sun yi nuni da cewar ganawar da shugaba Vladimir Putin na Rasha zai yi da Donald Trump a ranar Litinin mai zuwa ba za ta haifar da 'da mai ido ba sakamakon kamarin da rashin jituwar kasashen biyu ke ci gaba da yi daidai lokacin da Donald Trump ke ci gaba da fuskantar Allah wadai daga wasu kasashen na Tarayyar Turai sakamakon kutse cikin al'amuran gudanarwa kasashen da suka dade suna kawance da Amirka.