1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na ci gaba da sallamar jakadun waje

Mouhamadou Awal Balarabe
March 30, 2018

Gwamnatin Rasha ta sallami jami'an Diflomasiyyar kasar Holland a matsayin martini kan korar jami'an Diflomasiyyanta da Netherland ta yi bayan zargin yunkurin kisan tsohon jami'in asirin Rasha Serguei Skripal.

https://p.dw.com/p/2vFko
Russland Außenministerium in Moskau
Hoto: picture-alliance/dpa/Sputnik/M. Blinov

Rasha ta kuma dibar wa Birtaniya wa'adin wata guda don ta rage yawan jami'an diplomasiyarta a Rasha. Da hantsin wannan Jumma'a ne ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ta gayyaci jakadun kasashe tara na yammacin duniya a Moscow domin ta bayyana musu matakin da ta dauka a kansu bayan da kasashensu suka sallami jami'an diplomasiyyasar Rasha. Jakadan Jamus a Rasha na daga cikin wadanda aka gayyata, alhali yana daga cikin manyan jami'ai da suka yi fatan inganta dangantakar da ke tsakanin kasashensu bayan da aka nadashi.

Jami'an diflomasiyyar Amirka akalla 60 ne Moscow ta sallama tare ga rufe karamin ofishin jakadancin Amirkan. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewar za a iya fuskantar dawowar yakin cacar baka tsakanin kasashen yammacin duniyar da Rasha sakamakon zargin yunkurin kisan da ke kara zama dalilai na wargaza alakar kasashen duniya da Rasha.