1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba kan takaddamar Rasha da Ukraine

Abdourahamane Hassane LMJ
February 23, 2022

Kasashen yammacin duniya na ci gaba da mayar da martani tare da daukar mataki na hukunci, bayan da Shugaba Vladmir Putin ya amince da wasu yankuna biyu na Ukraine a matsayin masu cin gashin kansu.

https://p.dw.com/p/47UCK
Rasha I Sojojin Rasha na Fita daga Ukraine
A baya dai Rasha ta sanar da fara janye sojojinta daga kan iyakarta da UkraineHoto: AP/picture alliance

Kwararru da wasu shugabannin kasashen duniya sun yi ittifakin cewar da wannan sanarwa da shugaban na Rasha ya yi ta amincewa da wasu yankuna biyu na Ukraine a matsayin kasashe ma su 'yancin cin gashin kai, yana nufin cikin sa'o'i masu zuwa Rasha za ta kutsa kai a cikin Ukraine da nufin mamaye makwabciyar tata. Shugaban na Rasha Vladmir Putin ya sha alwashin kara karfafa rundunar sojojinsa na kasa da na sama da kuma na ruwa, wanda ya ce suna amfanin da fasahohin zamani masu inganci.
A shekarun baya-bayan nan dai Rashar ta kera wani makami mai linzami, wanda babu wani abin da zai iya yi masa garkuwa daga ko'ina a duniya. Duk da halin da ake ci dai Putin ya ce suna yin maraba da duk wata tattaunawa kan takaddamar tasu da Ukraine, sai dai ya ce muradun kasarsa sune kan gaba: "Kasarmu a ko yaushe a bude take domin tattaunawa kai tsaye da gaskiya, a shirye muke mu nemo hanyoyin diflomasiyya kan batutuwan da suka fi sarkakiya. Amma ina son nanata cewar, muradun Rasha da tsaron al'ummarmu abu ne da ba za a iya tantama a kansa ba.''

Ukraine I Takaddama I Donetsk I Rasha
Al'ummar Donetsk a Ukraine, sun yi gangami rike da tutocin RashaHoto: Alexei Alexandrov/AP Photo/picture alliance
Takaddama | Ukraine I Rasha I Putin
Shugaban kasar Rasha Vladmir PutinHoto: Sergey Guneev/Kremlin/Planet Pix/Zuma/dpa/picture alliance

Yanzu haka dai dakarun Rasha sun shiga yankunan Luhansk da Donetsk wanda ta amince da su a matsayin kasashe masu cikakken 'yanci. Hakan ya kara firgita kasashen duniya musamman Amirka wacce ta ce bayan takunkumin da ta saka ga Rashan, tana tunanin mataki na gaba. A yanzu haka dai wannan takkadama tsakanin Rasha da Ukraine ta shiga wani matsayi, wanda bisa ga dukkan alamu ya dagula yunkurin da shugabannin kasahen duniya ke yi na ganin an warware batun a siyasance.