Ranar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta wae | BATUTUWA | DW | 16.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Ranar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta wae

Majalissar Dinkin Duniya ta ware ranar 16 ga watan Oktobar kowacce shekara, domin tunawa da muhimmancin abinci ga rayuwar dan Adam a duniya.

Afrika Hungerkatastrophe Archivbild 2005

Sauyin yanayi da kwararowar hamada, na taimakawa wajen janyo karancin abinci

Abinci dai shi ne ginshikin rayuwa, kuma muhimancin abincin ga rayuwar dan Adam ya sa Majalissar Dinkin Duniyar ta ware wannan rana. Jihar Agadez a Jamhuriyar Nijar, jiha cé da ta bai wa noman rani muhimanci sosai, inda al'ummar da ke rayuwa cikinta ke sa mun wadataccen abinci mai gina jiki. Sai dai sauyin yanayi da ya haddasa ambaliya da kwararowar hamada, ya haifar da karancin abinci ga al'ummar wannan jiha, kasancewar a yanzu haka akwai iyalin da sai sun sha wahala suke samun abinci sau daya a wuni, inda watarana ma yake gagararsu.

 Karin Bayani:  Nijar: Martani kan ziyarar shugaban Areva

Kafa kamfanunnukan fitar da arzikin karkashin kasa da suka mamaye wuraren noma da kiwo a jihar ta Agadaz ma sun taimaka wajen haifar da matsalar karancin abincin.

Hilfslieferungen im Niger

Tsadar kayan abinci ka iya janyo karancinsa

Rage hauhawar farashin kayan abinci da kuma  yadda za a hada kai musamman tsakanin kasashe masu tasowa, ka iya taimakawa ainun wajen habaka hanyoyin samar da abinci injI Elhadji Mani Ayouba da ke saro kayan abinci daga kasar Aljeriya, wanda ya cé annobar COVID-19 ta kawo cikas sosai wajen shigowar da abinci jihar Agadez a bana.

 Karin Bayani: Bukatar tallafa wa jihar Diffa da abinci

Manoma  a fanni da dama na ganin gazawar hukumomi da kungiyoyi masu fada a ji a harkar noma , musumen ma idan a aka yi la'akari da yada talafi baya fado musu yada ya kamata ahaman elhadji  manomi ne da ambaliya ta rusta da chi domin ko ya rasa ganakan su. Ganin tasirin cimaka ga al'uma da ma yada tsarin nan na duniya mai bayar da abinci na PAM da ke karkashin Hukumar Abinci da Ayyukan Gona ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, a bana ya samu kyautar zaman lafiya da kungiyar kasa da kasa ke bayarwa ga zakakuran da suka yi aiki na gari. Haka kuma suma kungiyoyi masu zaman kansu na bayar da agajin abinci ga mabukata. Elhadji Bouba Abdou jami'in kungiyar Hed Tamat ya ce da talafin kasar Jamus, sun bayar da agaji sosai wajen samar da abinci ga al'umma. Duk wani kokari da DW ta yi na jin ta bakin ofishin gwamnati mai kula da fanin karancin abinci wato  Celule Crise Alimentaire, ya ci tura.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin