Agadez yana cikin biranen Jamhuriyar Nijar da ke da tasiri bisa siyasa, da tattalin arziki gami da al'adu.
Galibin mazaunan wannan yankin Azibinawa ne da sauran 'yan kasar da kuma baki daga kasashen ketere. Cikin shekarun da suka gabata Agadez ya zama hanyar da bakin haure 'yan kasashen Afirka ke bi domin kai wa Libiya da kuma Turai ta barauniyar hanya.