Putin ya yi kashedin barazana ga Rasha | Labarai | DW | 16.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Putin ya yi kashedin barazana ga Rasha

Shugaban na Rasha da ke wata ziyarar aiki a Belgrade, ya yi amfani da wannan dama wajan yin gargadi ga duk wani mataki na yi wa kasarsa barazana a rikicin Ukraine.

A cikin wannan ziyara dai shugaban na Rasha za iyi kokarin gina fada a jin da Rasha take da shi a zuciyar Turai. Daga kasar ta Sabiya, Shugaban na Rasha zai isa a birnin Milan na Italiya da yammacin wannan Alhamis, domin wasu jerin tattaunawa da shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko da kuma shugabannin Turai, a daura da babban zaman taron ASEM da zai hada shugabannin kasashen Turai da na Asiya daga ranar 16 da ran 17 ga wannan wata, inda za su yi kokarin samar da mafita a rikicin da ke tsakanin Kiev da 'yan awaren gabacin kasar ta Ukraine. A jiya Laraba ne dai Shugaba Poroshenko na Ukraine ya tattauna ta wayar tarho da Barack Obama na Amirka kan batun zaman lafiya a gabacin kasar ta Ukraine.