PDP ta soki lamirin dage zaben Edo | Siyasa | DW | 09.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

PDP ta soki lamirin dage zaben Edo

Jam'iyyar PDP da ke adawa a Najeriya da ma sauran jam'iyyun adawa na kasar sun nuna rashin amincewarsu da dage zaben jihar Edo da aka yi bisa dalilan tsaro.

PDP da sauran jam'iyyun adawa na kasar suka ce dage zaben a wannan loakcin bai dace ba domin kuwa an cika dukannin sharuda suka kamata wajen gudanar da zabe. Dr. Umar Ardo wanda jigo ne na jam'iyyar PDP ya ce APC ta hango rashin samun nasara shi ne ya sanya ta hada baki da hukumar zaben wajen daga zabe.

Baya ga 'yan siyasa, su ma masu sharhi kan lamuran yau da kullum a kasar na tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu inda wasunsu ke cewar hukumar zaben kasar ta INEC ta mika wuya ga jami'an tsaro hasalima su ne ke shata mata abinda za ta yi sai da INEC din ta ce ita hukuma ce mai cin gashin kanta.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da aka dage zabe a Najeriya bayan an kammala shiri na gudanar da shi don a shekarar 2015 ma an dage zaben shugaban kasa bisa abinda hukumar ta kira dalilai na tsaro, lamarin da 'yan adawa a wancan lokacin suka ce wata makarkashiya ce ta shirya magudi.

Sauti da bidiyo akan labarin