PDP ta soki lamirin daga zaben Edo | Siyasa | DW | 24.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

PDP ta soki lamirin daga zaben Edo

Jam'iyyar PDP da ke adawa a Najeriya ta soki hukumar zaben kasar ta INEC game da daga zaben gwamna na jihar Edo da ke kudancin kasar bisa dalilai na tsaro.

Jam'iyyar ta PDP wadda ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya kana dan takararta na daga cikin wadanda ke neman kujerar shugabancin jihar ta Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya. An dai bayyana cewar dalililai ne na tsaro suka sanya aka dage zaben amma kuma jam'iyyar PDP da ma sauran jam'iyyun adawa na kasar sun ce ba haka abin ya ke ba.

'Yan adawar suka ce gabannin dage zaben dai an shaida musu cewar an cika ka'idoji kimanin 11 daga cikin sha biyun da ake bukatar cikawa kuma sai daga baya suka ji an ce an dage zaben, lamarin da ya sanya suka ce akwai wata a kasa dangane da wannan batu. Wannan ne ma ya sanya suka yi Allah wadai da wannan mataki da aka dauka.

Guda daga cikin jiga-jigan jam'iyyar ta PDP Dr. Umar Ardo ya ce duk da wannan kulalliya da aka yi na dage zaben wadda ganinsu APC ce ta assasa shi, jam'iyyarsu shiye ta ke ta lashe zaben a lokacin da za a gudanar da shi nan gaba cikin wannan wata. Dr. Ardo ya ce tarihi ya nuna cewar duk jam'iyyar da ke kan mulki da ta yi yunkurin dage zabe to a karshe ba ta samun nasara.

A daura da wannan kuma, masu sharhi kan lamuran siyasa a kasar na da'awar cewar yanzu a Najeriya hukumomin tsaro ne ke nuni ga irin tafarkin da ya kamata a ce hukumar zabe ta bi wajen gudanar da zaben duba da irin abubuwan da suka faru a baya musamman ma lokacin zaben da aka yi na shugaban kasa a 2015, sai dai hukumar zaben kasar ta INEC a ko da yaushe ta na jaddada cewar ita mai cikakken iko ce.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin