Obasanjo: Al'umma su kare kuri'unsu | BATUTUWA | DW | 22.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Obasanjo: Al'umma su kare kuri'unsu

Yayin da shirye-shiryen tunkarar babban zaben Najeriya da ke tafe a cikin watan Fabarairu mai zuwa, jam'iyya mai mulki da masu hamayya na ci gaba da tallata manufofinsu ga masu kada kuri'a.

Nigeria Bildergalerie Staatspräsidenten Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo

Yayin da shirye-shiryen tunkarar babban zaben Najeriya da ke tafe a cikin watan Fabarairu mai zuwa ke cike da zarge-zarge daga bangaren hamayya, a daidai lokacin da jam'iyya mai mulki da masu hamayyar ke ci gaba da tallata manufofinsu ga masu kada kuri'a,gwmnatin tarayyar dai na zargin babbar jam'iyyar hamayya ta PDP da zama kanwa uwar gami wajen haddasa rikice-rikice a kasar musamman a daidai lokacin da mayakan Boko Haram ke kara farfadowa. Azantawarsa da DW tsohon shugaban Tarayyar Najeriyar Olusegun Obasanjo ya shawarci al'ummar kasar su tabbatar da yin zabe cikin tsarin da ya dace. 


Olusegun Obasanjo ka shawarci 'yan Najeriya da ma sauran kasashen Afirka su bi duk matakin da ya dace wajen bin kadinsu matukar aka murde musu zabe. Ko menene dalilinka na yin wannan kiran?

"Ko wanne tsarin doka da ma kundin tsarin mulki, akwai tanadin dokar yadda za a samar da mafita kan duk wani sabani ko wata tababa da aka fuskanta yayin zabe, wato dai akwai kotunan sauraron kararraki a matakai daban-daban, kama daga kotunan da aka saba gani ko na musamman da ake kafawa don sauraron korafe-korafen zabe ko ma kotun koli. Kuma da alama za su yi maraba da hakan. Saboda haka mu daina ganin baiken abin da muka cimma. Kuma a ganina ma zaben da aka warware takaddamarsa a gaban kotu ya fi ace ma kwata-kwata babu zaben."

Wahlen in Nigeria Warteschlange

Shirye-shiryen zabe a Najeriya

Shin ko kana jin damuwa da yadda zabukan baya-bayan nan suka cika da tashe-tashen hankula?

"Wannan yana da alaka da shugabanci, idan har shugabanni za su sanya a zukatansu cewa lallai nagarta ce abar bukata wajen shirya karbabben zabe, to ya zama wajibi mai neman jagorantar al'umma ya kasance mai burin mulkar su cikin adalci, sannan ya mutunta tanadin doka."

Ganin yadda Najeriya ke tunkarar wannan babban zabe a cikin watan gobe, ko menene hasashenka a matsayinka na tsohon shugaban kasa?

"Matukar aka kaucewa katsalandan da tsoma baki da murdiyar zabe, to ba shakka za mu samu zabe na gaskiya kuma karbabbe ga kowa."

Ko wanne sako ka ke da shi ga al'ummar Najeriya game da wannan zabe?

"Sakona ga 'yan Najeriya shi ne zabe na nan tafe, ku je ku kada kuri'a, ku kasance cikin shiri sannan ku kare kuri'unku, kuma da zarar an sanar da sakamako na gaskiya to ya zama wajibi mu karba mu amince da shi." 

Sauti da bidiyo akan labarin