1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran

Gazali Abdou Tasawa MNA
May 16, 2018

A daidai lokacin da EU ke kokarin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran, masana harkokin siyasar kasar na nuna fargabarsu a game da yiwuwar fadawar kasar da ma yankin Gabas ta Tsakiya baki daya a cikin tashin hankali.

https://p.dw.com/p/2xpjx
Belgien EU-Außenministertreffen
Hoto: picture-alliance/Photoshot

A taron da suka gudanar a ranar Talata a birninn Brussels tare da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammed Zarif, ministocin harkokin wajen kasashen Turai sun sha alwashin kare yarjejeniyar nukiliyar da kasar ta Iran ta cimma da kasashen duniya tare da daukar matakan kare tattalin arzikinta ta yadda kasar za ta dunga samun kudaden shiga ta hanyar sayar da man fetir da gas da Allah ya huwace ma ta. Kazalika kasashen na Turai sun sha alwashin ci gaba da yin huldar bankuna da ta zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa da kasar ta Iran tare kuma da samar mata da kudaden bashi da ma sauwaka hanyoyin zuwa saka jari a kasar kamar dai yadda Jean Yves Ledrian ministan harkokin wajen Faransa aka ambato yana mai cewa:

"Za mu yi nazarin hanyoyin kwantar wa da kasar ta Iran da hankalinta domin ganin ta samu sukunin cin moriyar sakamakon tattalin arziki wanda yarjejeniyar da muka cimma da ita a watan Yulin 2015 ta tanada."

To amma a wata fira ta musamman da ya yi da tashar DW Navid Kermani wani marubuci Bajamushe dan asalin kasar ta Iran ya bayyana cewa da wuya yinkurin da kasashen Turai ke yi na ceto ko kuma kare kasar ta Iran ya iya yin wani tasiri.

"A halin da ake ciki ban ga maganin da za su iya samar wa wannan ciwo na Iran ba, musamman ta la'akari da ake tunka da warwarewa tsakanin shugabannin na Turai, inda a misali shugaban Faransa ke kokarin hada kan Turai amma gwamnatin Jamus na nuna sanyin jiki da ma kokarin yi wa shugaban Faransar sabiya a tafiyar tasa."

Fargabar yiwuwar fadawar Iran cikin tashin hankali

Navid Kerman Navid marubuci Bajamushe dan asalin kasar Iran
Navid Kerman Navid marubuci Bajamushe dan asalin kasar IranHoto: picture-alliance/dpa/H. Kaiser

To amma Navid Kermani dan asalin kasar ta Iran wanda kuma ya saba kai ziyara a kai a kai tun bayan yarjejeniyar ta 2015 ya kara da cewa yanayin tattalin arziki da na zamantakewa ya tabarbare sosai a kasar, inda har yanzu masu ra'ayin rikau na addini ke rike da madafan iko. Kuma matakin Amirka na janyewa daga yarjejeniyar da irin matakan tattalin arzikin da ka iya biyo baya na iya jefa kasar da ma yankin baki daya a cikin tashin hankali.

"Yanayin tattalin arzikin kasar ba mai kyau ba ne, ga cin hanci ya kai koluluwar irin yadda ba a zata. Matalauta na cikin bacin rai musamman a tsakanin al'umma tsiraru a kasar wadanda a yau a shirye suke su ja ta tsage. Makamai na yawo ko ina a cikin kasar, zuciyoyin jama'a sun tafasa. A takaice dai za a iya cewa duk wasu alamu na fadawa halin da kasashen Iraki da Siriya da Afghanistan suke ciki sun kankama."

Kokarin kushe matakan da Trump ya dauka kan Iran

Ko a wannan Laraba ma dai shugabannin kasashen na Turai na gudanar da taro a birnin Sofia domin daukar matakan bai daya na kalubalantar matakin Shugaba Donald Trump na Amirka na janyewa daga yarjejeniyar nukiliyar ta Iran da neman saka mata takunkumin.

Abin fargaba ga kasar ta Iran dai a nan gaba shi ne tarzomar da 'yan kasar ka iya tayarwa sabili da matsin rayuwa da sukan iya shiga a sakamakon takunkumin da Amirka da wasu kawayen nata za su iya saka wa kasar a daidai lokacin da a share daya manyan abokanan gabarta a yankin wato Isra'ila da Saudiyya ke nan suna harararta daga nesa da kuma ke neman wata 'yar dama domin auka mata da yaki, wanda ka iya yaduwa a illahirin yankin na Gabas ta Tsakiya.