1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Narendra Modi zai je kasashen Gulf da Turai domin cinikayya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 11, 2026

Modi ya shawarci duniya ta alkinta cinikayyar zinariya da lu'u-lu'u, ta rage tafiye-tafiye, sanadiyyar tsadar makamashi.

https://p.dw.com/p/5Dbx0
Firaministan Indiya Narendra Modi.
Firaministan Indiya Narendra Modi.Hoto: ANI News/IMAGO

Firaministan Indiya Narendra Modi zai fara ziyarar aiki ta kwanaki biyar, a kasashen yankin Gulf da kuma na Turai, daga ranar 15 ga Mayu zuwa 20, a daidai lokacin rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara janyo tashin farashin albarkatun man fetur a duniya.

Karin bayani: Kasar Iran ta saki 'yan Indiya da ta kama

Mr Modi zai fara da Hadaddiyar Daular Larabawa, ranar Juma'a mai zuwa, inda za su tattauna da shugabanta ‌Mohammed bin Zayed Al Nahyan, kan musayar makashi, daga nan ya je Netherlands sai Sweden da kuma Norway, sannan ya zarce zuwa Italiya, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Indiya ta sanar a wannan Litinin.

Karin bayani: Trump ya sanar da kulla yarjejeniyar kasuwanci da Indiya

Bulaguron na Modi na da alaka da kudurinsa kan shawarwarin da ya bai wa kasashen duniya, na alkinta cinikayyar zinariya da lu'u-lu'u, sannan a rage yawaitar tafiye-tafiye, sanadiyyar tsadar makamashi da duniya ke fama da shi a yanzu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani