Indiya na taron koli kan fasahar AI
February 16, 2026
Gwamnatin New Delhi na shirin fara karbar bakuncin wani taro na yini biyar kan fasahar kirkira wato AI. Ana sa ran taron zai mayar da hankali ne kan zakulo amfanin fasahar da kuma matsalolinta, musamman yadda ake nuna damuwa kan makomar ayyukan yi da kuma tsaron yara. Kasar Indiya na kasancewa guda daga cikin kasashen da suka fi amfani da fasahar ta AI, bayan kasashen Amurka da China. Ma'aikatar fasahar Indiya ta ce taron zai taimaka wajen yin hangen nesa ga duniyar AI wanda ke amfanar da kowa, ba kawai wasu kamfanoni masu karfin ci gaba ba.
Karin bayani: Taron koli kan fasahar kirkira ta AI
A kalla baki 250,000 ne za su halarta da ma shugananin kasashen duniya 20 ciki har da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da kuma takwaransa na Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna shakku kan AI sakamakon yadda ake fitar da labaran kazon kurege da kuma faya-fayan bidiyo na bogi.