1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta nemi taimakon Jamus na kayan yaki da ta'addanci

February 19, 2026

A ci gaba da kokarin neman hanyar tunkarar matsalar tsrao, Najeriyar ta sake karkata ga kasar Jamus don neman daukin kayan yaki da 'yan ta'adda

https://p.dw.com/p/595MK
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Nigerian Presidency/Handout/Anadolu/picture alliance

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nemi jamus da ta tallafa wa mata da jirage masu saukar ungulu domin shawagi da tattara bayanai kan 'yan taädda a yankin Sahel. Sabuwar bukatar na zama ta baya bayan nan ga wata kasa ta waje bayan Amurka da kasar Turkiya.

Jamus dama ta jima tana taimaka wa sojojin Najeriya a kokarun inganta tsaro. Najeriya dai ta nemi Jamus ta tallafa da jirage masu sauka ta ungulu domin shawagi da tattara bayanai na 'yan ta'dda a daukacin yankin Sahel.

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz Hoto: dts-Agentur/picture alliance

Wata ganawa ta wayar tarho a tsakanin shugaban Najeriyar Bola Tinubu da shugaban Jamus Fredrich Mertz ta kare tare da Bola Tinubun neman agajin da ke iya tasiri a cikin babban yakin na ta'adda.

Wannan ne dai karon farko da shugabannin biyu ke share lokaci suna tattaunawa bisa batun tsaron da sannu a hankali yake jefa sunan Najeriyar cikin duhu.

Tun a 2012 ne dai Jamus ta fara bayar da agaji kan batun na ta'addanci. Kuma kama daga inganta bincike da kwakwafi cikin batun makamai, ya zuwa horaswa da musayar bayanai              Jamus din ta dade tana taka rawa wajen kare ta'addanci a Najeriya. Jamus din dai alal misali na taka rawa wajen horar da sojan Najeriyar kera makaman yaki.

Sojojin Najeriya a fagen yaki da 'yan Boko Haram
Sojojin Najeriya a fagen yaki da 'yan Boko HaramHoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

Kabiru Adamu mai sharhi kan batun tsaro yace sabon matakin na iya tasiri a kokarin tunkarar matsalar

Sabuwar bukatar da ke zuwa a lokacin da kasashen Amurka da kila ma Turkiya ke kara baiyana a sahun gaba, na da babban burin kawo sauyi cikin kasar da ke korafin rashin kayan yaki.

To sai dai kuma banbancin da ke cikin batun mulki a kasashen Sahel din na iya kawo cikas a cikin shawagin da kila ma tasirinsa a kokarin kare ta'addar.

Da kyar da gumin goshi ne dai Najeriya ta karbo wani jirgi da ya ratsa sararin samaniyar Burkina Faso ya kuma jawo muhawara mai zafi a tsakanin Abuja da mahukuntan Ouagadougou.

Jirgin Helikopter na sojin Jamus samfurin Airbus H145M
Jirgin Helikopter na sojin Jamus samfurin Airbus H145M Hoto: Julian Stratenschulte/dpa/picture alliance

Dr Kabir Sufi kwarrare a siyasar yankin da kuma yake fadin kokarin shiga Sahel din ya saba da zahirin da ke cikin yankin yanzu.

Kasar ta Jamus dai na zaman kasa ta uku a kasa da watanni guda uku da tarayyar Najeriyar ke tunkara cikin batun tsaron a wani abun da ke dada nuna alamun mai da kai zuwa ga agajin kasashen waje.

Yan kwanaki da kila watanin da ke tafe dai yan Najeriyar da daman gaske na zaman jiran tasirin agajin kasashen na waje a kokarin kai karshen ta'addar.