Najeriya: Rayuwa cikin fargaba a yankin arewacin Najeriya | BATUTUWA | DW | 27.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Rayuwa cikin fargaba a yankin arewacin Najeriya

A karon farko sarakunan gargajiya sun bayyana damuwa kan halin rashin tsaro da yankin arewacin Najeriyar yake ciki duba da tsawwalar hare-haren 'yan ta'adda da masu garkuwa da jama'a.

Nigeria Abuja Sultan Sokoto Sa'ad Abubakar III

Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III

Ga dukkan alamu tura ta kai bango kan batun rashin tsaro a tarayyar Najeriya bayan ya dauki hankalin sarakunan kasar irin su Sultan Sa'adu Abubakar  da ke zaman sarki mafi tasiri a sashen arewacin Najeriya inda ya ce yankin na Arewa na daukacin mamayar 'yan ina da kisa masu cin karensu ba babbaka.

Karin Bayani: Yawaitar kananan makamai a Najeriya

Sultan Sa'ad ya ce babu kasuwa ba wani kauye da masu aikata ayyukan ta'addanci ba su ratsawa a yankunan arewacin Najeriya, yana mai bayyana irin girman annobar ta 'yan bindiga da  kuma kamarin da matsalar tsaro  ke kara yi a Najeriya, wacce sarakuna da ma talakawan kasar na yankin Arewa ke cewa hakan na kan hanyar rusa daukacin kasar, a cewar Murtala Aliyu sakataren kungiyar dattawan arewacin Najeriya ACF.

Karin Bayani: Buhari ya magantu kan batun tsaro

Nigeria - Boko Haram Konflikt

Sojojin Najeriya a fagen yaki da Boko Haram

Kalaman basaraken na zuwa ne a daidai lokacin da wani rahoto cibiyar kula da ta'addanci ta duniya ke fadin har yanzu Najeriyar na zama ta uku mafi fuskantar annobar 'yan ta'adda a duniya. Kasa da sa'o'i 24 da suka gabata 'yan bindiga sun halaka wani basaraken gargajiya a Jihar Ondo, a ci gaba da hari da satar al'umma da na tabarbarewar tsaro a Arewa maso gabashin Najeriya  da ma daukacin sassan arewacin kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin