Najeriya: Kakkabe ′yan bindiga a Katsina | BATUTUWA | DW | 20.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Kakkabe 'yan bindiga a Katsina

Sakamakon umarnin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar na kakkabe 'yan bindiga a jihar Katsina, ita ma rundunar 'yan sandan kasar ta kaddamar da yaki da 'yan bindigar a jihar.

Symbolbild | Nigeria | SWAT

Kokarin kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a Katsina

Rundunar 'yan sanda kasar ta ce wannan karan ta yi shirin da ba ta taba yi ba na murkushe 'yan ta'addan, inda aka samar wa jami'an runduna ta musamman da ke yaki da 'yan bindigar wato SARS isassun kayan aiki. Sai dai a na ta bangaren gwamnatin jihar Zamfara ta ce kamata ya yi gwamnatin tarayya ta yi shirin yakar 'yan bindigar na bai daya, saboda yanzu haka 'yan sun fara afkawa yankunan jihar. 

Tun bayan da gwamnatin tarayya ta dauki aniyar kakkabe 'yan bindigar a jihar Katsina, al'umma ke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu. Hare-haren 'yan bindigar dai ya janyo asarar dimbin rayuka da dukiyoyin al'umma a jahohin Arewa maso Yammacin Najeriyar, abin da ke sanya tsoro da fargaba ga mazauna jihohin da abin ya yi kamari da ma wadanda ke makwabtaka da su. 

Sauti da bidiyo akan labarin