Matsalar rashin tsaro na kara yin kamari a arewacin Najeriya | Labarai | DW | 16.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar rashin tsaro na kara yin kamari a arewacin Najeriya

'Yan bindiga sun halaka mutane guda 30 a wani harin da suka kai a arewa maso gabashin Najeriya.

Mutanen wadanda ke bisa babura su kusan guda goma sun kai hare-haren a kauyukan Tsauwa da Dankar da ke cikin Jihar Katsina inda suka yi harbin kan mai uwa da wabi a kan jama'a suka kashe mutane 30. Kakakin 'Yan sanda na Katsina Gambo Isa ya ce 'yan bindigar sun kashe mutane 21 a Tsauwa kafin su harbe tara a Dankar. Gwamnatin Jihar Katsina ta baza 'yan sanda a kauyukan wadanda suka soma gudanar da bincike, tuni da suka kama wani mutumin da ake zargi yana daga cikin maharan.