Najeriya: Buhari ya magantu kan batun tsaro | BATUTUWA | DW | 14.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Najeriya: Buhari ya magantu kan batun tsaro

A yayin da Tarayyar Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro, shugaban kasar ya bayyana aniyarsa ta samar da daukacin bukatun jami'an tsaro, a yayin taron majalisar tsaron kasar da nufin tunkarar matsalar.

Bombenexplosion Polizei in Nigeria

Shirin tunkarar matsalar tsaro a Najeriya

Duk da cewar dai sojojin Najeriyar na ikirarin samun galaba a kan kungiyoyin ta'adda a yankin Arewa maso Gabas na kasar, can a Arewa maso Yamma dai batun rashin tsaron na dada kamari inda yan ina da kisa ke ci gaba da cin karensu har gashinsa. Wani rahoton hukumar kula da 'yan gudun hjira ta Majalisar Dinkin Duniya dai, ya ce kusan mutane dubu 23 ne suka tsallaka ya zuwa Jamhuriyar Nijar daga jihohin Zamfara da Katsina da kuma Sokoto cikin tsawon wata guda, domin tsira daga karuwar ayyukan 'yan ina da kisan da ke tashi da lafawa a cikin yankin.

Ya za a kawo karshen matsalar?

Kuma ko a wannan mako dai 'yan ina da kisan sun yi nasarar tayar da kauyuka da daman gaske  a jihar Katsinan bayan ta'azzarar hari a Kaduna, a wani abun da ke kara nuna irin jan aikin da ke gaban 'yan mulkin na Abuja. Mansur Ali Mashi dan majalisar wakilan kasar ne daga Katsina, kuma ya ce shugaban kasar na da bukatar sauyin taku a cikin neman tunkarar rikicin da ke kara ta'azzara a halin yanzu.

Nigeria Selbstmordanschlag in Zabarmari

Kisan ba gaira a Najeriya

To sai dai kuma ko wacce dabara Abujar ke shirin dauka da nufin tunkarar matsalar, yayin wani taron majalisar tsaron Tarayyar Najeriyar da aka gudanar a Abuja, shugaban kasar ya yanke hukuncin bai wa jami'an tsaron daukacin kayan aikin da suke bukata da nufin  tunkarar matsalar da ma ragowar rashin tsaron da ke cikin kasar a halin yanzu. Babban mashawarcin tsaron kasar Babagana Monguno ya ce  gwamnatin kasar ta damu, sannan kuma tana shirin daukar dukkan matakai da nufin warware matsalar da ke neman komawa zuwa wutar daji yanzu. 

Matsalar tattalin arziki

Wannan matsalar dai, na zuwa ne bayan karyewar jerin yarjejeniyoyin da jihohin yankin suka kulla a tsakaninsu da masu kisan da nufin tabbatar da zaman lafiyar al'umma. Duk da rahotannin samun galaba akan 'yan ta'addar yankin Arewa maso Gabas da ke ji a jiki a hannun sojoji na kasar a halin yanzu, akwai dai tsoron ta'azzarar ayyuka na 'yan ina da kisan na Arewa maso Yamma, na iya shafar harkokin noma da na kiwo a cikin kasar da ke fatan komawa noma bayan rushewar tsarin man fetur. Matsalar ta tsaro da annobar COVID-19 da ta jawo rushewar tattali na arzikin kasar dai, na barazanar jefa kasar cikin halin ni 'yasu.

Sauti da bidiyo akan labarin