Sulhu da ′yan bindiga ya inganta tsaro a Zamfara | Siyasa | DW | 17.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sulhu da 'yan bindiga ya inganta tsaro a Zamfara

'Yan bindiga da dama sun mika makamansu ga jami'an tsaro bayan da gwamnatin Zamfara ta yi yunkurin yin sulhu da su. Wannan mataki da ke gudana a wurare dabam-daban na jihar ya kawo lafawar kai hare-hare.

Masana tsaro da dama a Najeriya na ganin sasantawar a matsayin hanya daya tilo ta kawo karshen kashe-kashen al'umma da ake yi a jihar Zamfara. Gwamnatin jihar ta himmatu gadan-gadan tare da hada gwiwa da jami'an tsaro.  SP Shehu Muhd shi ne kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara ya ce :"An gudanar da ganawa guda uku, hudu har zuwa biyar a nan babban birnin jiha domin kara tabbatar da cewa wannan yunkurin da aka dauko na sasantawa ya dore , kuma zaman lafiyar da aka fara samu ya dore. Kwamishinan 'yan sanda na jihar ya fadada wannan ganawa zuwa masarautu da ke fadin jihar ta Zamfara"

To ko me 'yan bindiga ke so a yi musu bayan mika makamai? Muhammad kiruwa Shi ne shugaban kungiyar Miyetta Allah na kasa kuma shi ne ke wakiltar Fulani a duk inda aka je sasantawa. Ya ce: "A saya mana dusa, a taimaka wa mutanenmu da suka yi asara, a tallafa musu kuma a sa 'ya'yansu makaranta su yi karatu da wadannan kudi."

Nigeria Viehdiebstähle in ländlichen Regionen (DW/Katrin Gänsler)

Makamai da dama 'yan bindiga suka mika a Zamfara

 Wasu 'yan bindigar da suka rika halaka mutane kafin su tuba kamar Muhammadu Bello ya ce yana da masaniyar duk abin da ake yi tun daga lokacin su Buharin Daji, abin da ya ce babu wani abu da yake boye a gareshi. Ya ce "Abin da muke so mu fada wa mutane su yi hakuri, abubuwa ne da Allah ya kawo karshensu. Mun dauki alkawari mun bari kuma ba za mu kara yi ba"

Baya ga jihar Zamfara da ke fama da hare-haren 'yan bindiga, akwai wasu jihohin da ke makwabtanta da ita da suke cikin wannan hali, abin da sakataren gwamnatin jihar Katsina kuma shugaban kwamitin sasantawa tsakanin Fulani makiyaya da manoma ya bukaci jihohin su yi sasantawa ta bai daya don gudun a yi baya ba zani. Ya ce :"Idan Zamfara za su yi, Kaduna za su yi, mu ma mu yi to za'a samu saukin lamarin. Gwamnoninmu na magana kuma na san za su samu hanya guda daya."

Sakamakon yunkurin wannan sasantawar dai, al'ummar jihar Zamfara sun fara samun sawabar 'yan bindiga.

Sauti da bidiyo akan labarin