1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kayayyaki na kara tsada

February 16, 2024

Duk da jerin matakai da hukumomin Najeriya ke dauka na dakile hauhawar farashin kayayyaki a kasar har yanzu ana samun tashin farashin da ke sanya fargaba a zukatan talakawa

https://p.dw.com/p/4cUuC
Hada-hada a birnin Lagos na Najeriya
Hada-hada a birnin Lagos na NajeriyaHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture alliance

Wata sabuwar kiddidiga a tarryar Najeriyar ta ce kasar na fuskantar hauhawar farashin abinci da makamashi da kaso daya cikin dari tsakanin watan Disamba na 2023 zuwa watan Janairu 2024

Hukumar ta ce hauhawar ta karu da kaso 28.9 cikin watan Disamban bara ya zuwa kaso 29.9 a Janairun bana, adadin da ke zaman mafi girma cikin kasar a shekara da shekaru.

Tun a wata Satumban da ya shude ne dai  Abujar ta ayyana dokar ta baci kan batun Abinci, sai dai kuma sai a cikin makon da ya gabata ne hukumomin kasar suka sanar da wani shirin samar da ton 42,000 na abincin.

Karin Bayani: Farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya

Babban bankin Najeriya CBN
Babban bankin Najeriya CBN

Shi kansa babban bankin kasar CBN na kokawar inganta dalar da yace tana kara yawa cikin kasar a halin yanzu, amma kuma al'umma na kallon rushewar kasuwannin canjin

Akalla dalar Amurka kusan miliyan dubu biyu ne bankin ya ce sun shigo kasar cikin makon da ya shude, amma kuma suka gaza tasirin da yan kasar ke fatan gani.

Ya zuwa wannan ranar dai dalar ta haura Naira 1,600 kan kowace dala, adadi mafi rushewa a daukacin tarihinta.

Dr Isa Abdullahi kwarrare kan tattalin arziki ya ce ana da bambancin gaske  tsakanin fada da kokarin cikawa a bangaren hukumomin wajen neman mafitar rikicin mai tasiri.

Karin Bayani: Taron neman hanyar magance matsalar abinci

Takardun kudin Dalar Amurka
Takardun kudin Dalar AmurkaHoto: Karel Navarro/AP Photo/picture alliance

Dabarbaru ko gazawar gwamnati, CBN dai ya ce yana da burin rage hauhawar zuwa kaso 21.4 kafin karshen shekarar 2024.

Duk da cewar dai tun cikin watan Oktoban da ya shude ya zamo gwamnan bankin, har ya zuwa yanzu Oluyemi Cardoso bai kira babban taron nazarin manufofin kudin kasar da ke cikin rudani ba. A fadar Yusha'u Aliyu mai sharhi kan tattalin arzikin kasar CBN din na taka rawa wajen rushewar batun kudin dama wadatar ta abinci.

Ya zuwa yanzun dai hauhawar farashin na neman rikidewa zuwa barazanar zaman lafiya a tarrayar Najeriya, kasar da tuni shugaban addinai da kabilu suke fadin ana bukatar gyara da nufin kaucewa zuciyar mai tsumma.