1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aiki kan tsadar rayuwa a Najeriya

Zainab Mohammed Abubakar
September 5, 2023

An shiga yajin aikin adawa da sauye-sauyen da shugaban Najeriya ya yi, da nufin farfado da ci gaban tattalin arzikin kasar wanda ya janyo matsalar tsadar rayuwa.

https://p.dw.com/p/4Vyit
Najeriya | Abuja | Yajin Aiki
Kungiyar kwkadagon Najeriya ta fara yajin aiki, domin adawa da sauye-sauye a kasarHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Tun ranar Juma'a ce dai Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC mai wakiltar miliyoyin ma'aikata a mafi yawa sassan kasar ta Afirka ta Yamma, ta yi kira da a shiga yajin aikin kwanaki biyu a shirye-shiryen shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar 21 ga watan Satumba. Bola Tinubu wanda ya gaji tattalin arziki mai rauni tare da basussuka da yawa da hauhawar farashin kayayyaki, ya yi watsi da tallafin man fetur mai farin jini, amma mai tsada wanda ya sa farashin lita ya ninka fiye da sau uku. Ya kuma dage takunkumin da ya janyo karin rushewar takardar kudi ta Naira.