1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin sabuwar Naira na tada hankali

February 7, 2023

An kasa samun mafita a ganawar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da gwamnoni da shugaban babban bankin kasa CBN kan matsalar chanjin sabuwar Naira.

https://p.dw.com/p/4NCXg
Shugaban bankin CBN Godwin Emefiele da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Hoto: Sodiq Adelakun/Xinhua News Agency/picture alliance

Ya zuwa juma'ar da ke tafe ne dai wa'adin da gwamnatin kasar ta diba domin tsomin shugaban kasar ya tsoma baki ke karewa, wa'adin kuma da har ila yau ke zuwa karshen  lokacin canjin kudade a kasar.

To sai dai wata ganawa a tsakanin shugaban kasar da gwamnan babban bankin da wasu shugabannin kungiyar gwamnonin kasar guda biyu da shugaban hukumar EFCC ta kare a Abuja ba tare da sanarwar da 'yan kasar ke fatan su ji ba.

Shugaban dama dai ya yi alkawarin sauraron bangarorin rikicin kafin yanke hukunci a kan batun da ya raba kawunan 'yan siyasar da ke kallon manufar ta fuskoki daban daban.

Naurar cire kudi ATM a Lagos
Hoto: Olisa Chukwumah/DW

Sai dai kuma ko a cikin zauren taron majiyoyi sun ce baki ya zo kusan daya a tsakanin gwamnan babban bankin da shugaban gwamnonin kasar Aminu Tambuwal da ke goyon bayan kai karshen karin wa'adin, da kuma shugaban gwamnonin jam'iyyar APC ta masu neman karin.

Karuwar hari kan kaddarorin bankuna a kasar da kuma kame jami'an da ke musu aiki ya tilasta akalla bankuna biyu Zenith da First Bank rufe harkokinsu har sai abin da hali ya yi.

Sannu a hankali dai  tafasar na shirin konewa cikin kasar inda hakurin bangarorin rikicin ke neman karewa tare da nuna alamun jan daga a tsakanin bangarorin biyu.

Wasu jam'iyyun 14 dai sun yi barazanar kaurace wa zaben idan har aka daga lokacin sauya kudaden da nufin kauce wa abin da suka kira kokarin sayen kuri'a yayin zaben.

Sabbin takardun kudin Naira na Najeriya
Hoto: Ubale Musa/DW

To sai dai daga dukkan alamu an samu barraka ko a tsakanin jam'iyyun 14 inda SDP ta ce bata goyon bayan kokarin janyewa daga zaben. A fadar shugabanta Shehu Gabam dake fadin ta yi baki ta kuma lalace yanzu.

Ko bayan batun taka rawa cikin siyasar kasar dai, shi kansa yadda zaben yake shirin gudana na fuskantar cikas sakamakon sabon matakin da ake kallon karuwar rashin kudi a ko'ina.

Hon Magaji Dau Aliyu dan majalisar wakilai ne da ke cewa dimukuradiyyar kasar na cikin hadari sakamakon yanayin da kasar ta shiga a halin yanzu.

Rudanin dai daga dukkan alamu ya tsallaka zuwa sashen shari'ar kasar inda wata kotu a Abuja ta haramta wa gwamnatin tarraya da babban bankin kasar karin wa'adin, a yayin kuma da wasu jihohin kasar guda uku ke zaman jiran fassarar kotun koli bisa abin da suke yi wa kallon haramcin gwamnatin kasar kan batun kudin.

Barrister Buhari Yusuf wani lauyan da ke zaman kansa a Abuja ya ce babu rudani cikin abin da ke faruwa a yanzu.

Ko ma wane mataki Abujar ta ke shirin dauka kan batun sauyin kudin dai daga dukkan alamu yana shirin yin tasiri ga makomar siyasar da ke dada nuna alamun mutuwa ko yin rai cikin kasar a halin yanzu.