1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fargabar karancin abinci a Najeriya

September 5, 2020

A wani abun da ke zaman barazana mai girma ga kokarin Najeriya na wadata kai da abinci, ambaliyar ruwa da ayyukan masu ta'adda da ma hauhawar farashi na neman jefa kasar cikin karacin halin Abinci.

https://p.dw.com/p/3i1Qd
Nigeria Homosexualität Polizei-Razzia in Lagos
Tsadar kayan abinci na haifar da fargabar matsalar yunwa a NajeriyaHoto: Reuters/T. Adelaja

Tuni dai mahukuntan Tarayyar Najeriyar suka zargi dillalai da masu neman riba da karuwa ta farashin na abinci da ya ninka kusan sau biyu cikin kasa da wattani uku a kasar. Najeriyar da a baya ta yi nisa cikin shirin wadatar da abinci tsakanin miliyoyi na yan kasar, daga dukkan alamu  na fuskantar mi'ara koma baya tsakanin talakawa na kasar da ke dada fuskantar barazana mai girma ta  fargabar karancin abinci sakamakon ta'azzarar matsalar tsaro tashe-tashen hankulan da ke zaman ruwan dare gama duniyar arewacin kasar da ambaliyar da ke zaman ta ba zata. A jihar kebbi kadai dai kusan hekta Miliyan daya ta shinkafa ne dai aka  kirga asara ko bayan wasu kananan hukumomi guda  hudu a Jigawa da ambaliyar ta kai ga shanye amfaninsu. Da ma tuni 'yan ina da kisa suka yi nasarar tsayar da sana'ar noman a jihohi da yawa da ke yankin Arewa maso Yamma da kuma Tsakiyar kasar. 

Nigeria Reis-Produktion
AMbaliya ta janyo asara ga manoman shinkafa a NajeriyaHoto: Imago Images/photothek/T. Imo

Najeriyar dai ta share shekarar da ta shude a matsayin kasa ta farko ga batun noman shinkafar a nahiyar Afirka dai, ga dukkan alamu na shirin fuskantar komawa ya zuwa tsohuwa ta al'adar shigo da abinci sakamakon barazanar da ke iya kai wa ya zuwa yunwa a gaba.

Karin Bayani: Shugaba Buhari ya kalubalanci manoman Najeriya

Ya zuwa  yanzu dai farashin na abinci ya yi tashin gwauron zabin da kasar ta jima ba ta ga irinsa ba a cikin yanayin rashin kudi na corona da karuwar farashin makamashi.

Karin Bayani: Masara ta bi sawun shinkafa a Najeriya

Buhun shinkafa dai na kusan Naira dubu 27 maimakon dubu 17 da yake wattani biyu baya. A yayin da ita ma masara ta kai kusan Naira dubu 20 daga Naira dubu takwas da ta faro a cikin kakar da ta shude. An dai ruwaito shi kansa shugaban kasar Muhammadu Buhari na adawa da karin farashin da ya ta'allaka da masu kasuwar da ke saye domin boye wa, a wani abun da ke nuna irin jan aikin da ke gaban 'yan mulkin masu fatan ci da kan amma a cikin halin sauki a tsakanin al'umma ta kasar. Mallam Garba Shehu dai na zaman kakaki na gwamnatin da ya ce Abujar na daukar jeri na matakai da nufin tabbatar da samun saukin tsadar da ke barazana ga rayuwa cikin halin kunci. Kyale kasuwar zama alkali a cikin harkar ta abinci dai na nufin kara tabarbarewa ga rayuwa ta 'yan kasar da sannu a hankali, suke fuskantar radadi na rayuwa ta jari hujja sakamakon cire tallafin mai da makamashin da ke dada kuna a zuciyar al'umma yanzu.